Peter Obi Yayi Magana Akan Babbar Hanyar Legas Zuwa Calabar.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na 2023, Mista Peter Obi, ya bayyana cewa aikin babbar hanyar Legas zuwa Calabar , duk da cewa yana da fa’ida, ba shi ne abin da kasa ta sa a gaba ba a yanzu.
Obi ya bayyana hakane ta shafinsa na X, yayin da yake mayar da martani game da makudan kudaden da aka cire domin aikin hanyar.
Ministan ayyuka Engr. Dave Umahi, ya bayyana aikin a matsayin daya daga cikin manyan ayyuka na kasa da kasa mai muhimmanci, inda ya tabbatar da dalilin da ya sa aka bayar da aikin titin/ layin dogo wanda ya ce shi ne titin jirgin kasa guda 10 .
obi yace Babban abin da ke damun ni shi ne batun manyan titunan da ba a kammala su ba a ko’ina a fadin kasar nan, wadanda da yawa daga cikinsu sun zama tarkon mutuwa da kuma hadarin tsaro.
“Abin takaici ne ganin halin da ’yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba, ke bi ta wadannan baraguzan hanyoyi a cikin mawuyacin hali, da fargabar haduwa da masu garkuwa da mutane da sauran hadura.
“Yawancin wadannan hanyoyi, masu mahimmanci ga ci gaban tattalin arziki, da ci gaban gaban al’umma gaba ɗaya, an yi su ne na shekaru da dama a yanzu kuma an gaza gyara sakamakon rashin kyakkyawan tsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *