Tsohon Saurayin Amarya ya aikewa sabon angonta hotunanta na lalata, aure ya mutu a daren farko

A daren farko ya mutu yayinda ake tsakiyar shagalin biki lokacin da Ango ya smau sakon hotunan Amaryarsa na irin lalatan da tayi a shekarun baya kafin su hadu.

Shafin LISA ya ruwaito cewa angon ya samu wasika tattare da katin Memory da wani ya turo yana zargin Amaryar da kasance mutuniyar banza.

Hakan ya sa Angon ya hanzarta wajen kallon abinda ke cikin Memorin.

Ango ya shiga daki idan ya gano wani tsohon saurayinta ne ya aiko da sakon cike da hotunansu na da suna badala.

Wannan abu bai yiwa angon dadi ba kuma take ya yanke shawarar kawo karshen shagalin da ake yi.

Kai tsaye Angon ta danna mata saki.

Daga baya Amaryar ta bayyana cewa lallai sun yi soyayya da tsohon saurayin amma daga baya suka fahimci cewa basu dace da juna ba. Sai ta yanke shawarar watsi da shi tunda iyayenta sun sama mata sabon saurayin da ya dace da ita.

Ta kara da cewa tsohon saurayin ya bukaci ta kawo ziyara gidansa ana sauran yan kwanaki da aure amma tayi banza da shi. Ta ce ba ta son ta sake maimaita irin kura-kuran da tayi a baya saboda tana son fara sabuwar rayuwa da mijinta.

Ashe wannan abu bai yiwa tsohon saurayin dadi ba inda ya fara dura mata ashariya kuma yayi alkawarin tona mata asiri.

KALMA TA MUSAMMAN ITACE: UNITY

5 Replies to “Tsohon Saurayin Amarya ya aikewa sabon angonta hotunanta na lalata, aure ya mutu a daren farko”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *