Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

Gwamnan jihar Kamo, Dakta Abdullahi Ganduje, yace tuni aka fara kokarin sulhu tsakaninsa da tsagin jam’iyyar APC ƙarƙashin Malam Shekarau.

Dailytrust ta ruwaito cewa jami’iyyar APC ta tsage gida biyu a jihar Kano, inda shugabanni jam’iyya guda biyu suka bayyana bayan taron gangami na jiha.

Sai dai gwamna Ganduje ya ƙara jaddada cewa uwar jam’iyya ta ƙasa ta amince da shuhaban APC na jihar Kano, wanda ya fito daga tsaginsa, Abdullahi Abbas.

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar, jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa, Ganduje yace, “siyasa ta gaji sulhu.”

Haka zalika gwamnan ya yaba wa kwmaishinoninsa da sauran mambobin majaisar zartarwa bisa namijin kokarinsu a wurin zaɓen na ranar Asabar.

One Reply to “Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *