Obasanjo Ya Baiwa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Lamunin Dalibai.

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya baiwa Shigaba Bola
Tinubu shawara kan lamunin dalibai.
Olusegun Obasanjo ya bukaci a sanya daliban jami’o’i masu zaman kansu a
tsarin domin tallafa musu.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin wani taro a Jami’a Bells
dake Ota a jihar Ogun
Obasanjo yace yana tsoron yadda wannan lamari na bashin dalibai zai samu
nasara ba tare da cin hanci ba
Tsohon shugaban kasar yace wannan tsari zai taimaka matuka wurin
cigaban Najeriya da kuma walwalar ‘yan kasar.
Sai dai yace cire wani bangare ko kuma wani sashi na mutane zai kawo
cikas wurin tabbatar da tsarin ya samu karɓuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *