JAN HANKALI AKAN HALI DA AKA SAMU KAI AKAN HUKUMAR HISBA

Murabus din Babban kwamandan Hisbah, Sheik Aminu Ibrahim  Daurawa abin dubawa ne, da ya kamata Dattawan Jahar Kano su bawa kulawa tare da samar da mafita akai.
 
Ya na da kyau mu tunatar da junanmu cewa dukkanin wani abu na alheri zai iya samun kutse daga shedan, kuma mafi yawan lokuta rashin jituwa kan samo asali ne daga rashin fahimta.
 
Kamar yadda mai girma gwamna ya taba fada a kwanakin baya, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai sauraron shawarwarin al’umma musamman ma Dattawa da malamai akan duk wani lamari da ya shafi tafiyar da mulkin jihar Kano.
 
To tunda Bahaushe ya ce “Kai da kaya duka mallakar wuya ne”  wannan kalubale ne ga wadannan rukuni na al’umma wato Dattawa  da kuma Malamanmu da ya wajaba su sauke nauyin da Gwamna ya dora musu na neman shawarar su, ta hanyar shawartar Gwamnati walau a sarari ko a boye dangane da abin da su ke ganin anyi ba daidai ba, a maimakon mayar da hankula zuwa shafukan sada zumunta ana sharhi da sauran zantutunkan da ba za su zamar wa wannan jihar alheri ba.
 
A yayin da al’umma ke fama da matsin rayuwa, a kuma  daidai wannan lokacin da Azumin watan Ramadan ya  kara karatowa, kamata yayi mu mayar da hankali wajen taimakon juna da nuna jin kai kar mu bari shedanu su sami dama akanmu.
 
Muna addu’ar Allah SWT ya zaunar da jihar mu da kasar mu lafiya, ya kawo mana karshen matsin rayuwa da mu ka samu kai, ya dawo mana da arzikin kasar mu, ya kuma yiwa shugabannin jagoranci bisa abinda ya ke shine daidai.
 

One Reply to “JAN HANKALI AKAN HALI DA AKA SAMU KAI AKAN HUKUMAR HISBA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *