Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam’iyya saboda abu daya

Jam’iyyar APC reshen jihar Ondo, ta dakatar shugabanta na ƙaramar hukumar Ifedore, Mista Alex Oladimeji, bisa zarginsa da cin amanar jam’iyya.

Punch ta bayyana cewa matakin dakatarwan na ƙunshe ne a wata wasika mai ɗauki da sa hannun mambobin kwamitin zartarwan APC a yankin.

Shugabannin APC na yankin, sun bayyana ƙarara cewa ayyukan da Oladimeji yake yi kwanan nan sun yi hannun riga da kundin dokokin jam’iyya.

Wani sashin takardar yace:

Mu mambobin kwamitin zartarwa na ƙaramar hukumar Ifedore mun dakatar da Alex Akinyemi a yau 3 ga watan Nuwamba, 2021 daga jam’iyyar mu APC.”

“Mun ɗauki wannan matakin ne sakamakon ayyukan cin amana da Anti-Party da yake yi wanda ya saba wa kundin dokokin jam’iyya.”

Shugaban jam’iyyar APC a jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya bayyana cewa babu wani rikici da jam’iyyar APC ke fama da shi a kowane mataki na jihar.

Ya kuma kara da jaddada cewa idan ma akwai wata matsala ta cikin gida a kowace ƙaramar hukuma ce, to APC tana da hanyoyin warware ta.

Yace:

“A halin yanzu da nake magana daku, jam’iyyar APC a jihar Ondo na ɗaya daga cikin reshen dake zaune lafiya a faɗin Najeriya.”

“Muna da hanyoyin warware matsalolin mu na cikin gida a matakin jiha har zuwa gunduma, saboda haka rikicin Ifedore zai zama tarihi.”

Duk wani koƙari na jin ta bakin shugaban da aka dakatar ya ci tura, domin wayar salulan shi bata shiga, kamar yadda TVC news ta ruwaito.

One Reply to “Jam’iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam’iyya saboda abu daya”

Leave a Reply to Babagana ibrahim Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *