Dakarun Hisbah sun yi ram da mata masu zaman kansu 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Aminiya ta rahoto cewa Dakarun hukumar Hisbah sun damƙe mata masu zaman kansu 44, tare da kwace kwalaban Barasa sama da 600 a faɗin jihar Jigawa.

Kwamandan Hisbah na jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru Garki, shine ya sanar da haka a ofishinsa, yayin da yake fira da manema labarai.

A cewar kwamandan jami’ai sun samu wannan nasara ne cikin makonni biyu, kuma da taimakon sauran hukumomin tsaro.

Bugu da ƙari Malam Garki ya bayyana cewa jami’ai sun yi wannan kamen ne a garuruwa 17 dake faɗin jihar.

A jawabinsa, kwamandan yace:

“Mun yi ram da mata masu zaman kansu 44, kuma mun cafke wasu mutum uku dake sana’ar siyar da barasa, sannan mun kwato katan 57 na barasa a hannun su.”

Ya kuma kara da cewa hukumar Hisbah ta miƙa mutanen ga rundunar yan sandan jihar domin gudanar da bincike da ɗaukar matakin doka.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa Hisbah ta gudanar da wannan aikin ne biyo bayan umarnin gwamnatin jihar Jigawa na garƙame wuraren siyar da barasa da wuraren baɗala.

A cewarsa har yanzun dokar haramta sha da kuma sana’ar miyagun kwayoyi na nan tana aiki a faɗin jihar.

Daga ƙarshe, ya roki al’ummar jihar Jigawa da su cigaba da baiwa Hisbah haɗin kai, ta hanyar taimaka musu da bayanai domin kawo ƙarshen masu wannan halayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *