Laifi Ne Hana Jami’anmu Gudanar Da Ayyukansu_EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yi gargadin, cewa laifi ne mutum ya hana jami’anta gudanar da ayyukansu.
Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba, ya ce gargadin ya zama dole a kan yadda mutane da kungiyoyin da hukumar ke bincike ke daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar ‘yan baranda domin hana hukumar ta EFCC gudanar da ayyukan ta.
Ya ce, “A lokuta da dama, jami’an hukumar suna yin taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan hargitsi domin kaucewa tabarbarewar doka da oda. saidai kuma abin takaici ana ɗaukar irin wannan halin a matsayin raunin hukumar.
Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba, don haka za a fuskanci hukuncin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *