Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa EFCC Ta Yi Jankunne Yayin Da Ake Mata Katsalandan a Harkokin Ta.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya yi ta yin katsalandan kan harin da jami’an EFCC suka kai gidan sa na Albuja ba bisa ka’ida ba.
Bello, a wata sanarwa da ya fitar daga ofishin yada labaransa, ya koka da cewa Najeriya ba kasa ce mai bin doka da oda ba, yana mai nuni da cewa akwai wata doka da wata babbar kotu da ke Lokoja ta bayar na hana hukumar kama shi har sai an yanke hukuncin karshe na wani babban kotun da ya shigar da karar.
Hukumar EFCC, a ranar Laraba, ta tura jami’anta zuwa gidan Bello na Abuja da nufin kama shi.
Sai dai babban jami’in yada labarai na hukumar, Dele Oyewale, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba a Abuja, ya bayyana cewa: “Hukumar EFCC na son gargadin jama’a cewa laifi ne na hana jami’an hukumar yin aikinsu .
“Sashe na 38 (2) (a (b) na dokar kafa hukumar EFCC ya nuna cewa an hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu yanda ya dace, wadanda suka aikata laifin na fuskantar hukuncin zaman gidan yari na kasa da shekaru biyar.
“A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan hargitsi don gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana ɗaukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni.
“Saboda haka, hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta amince da duk wani yunkuri na wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba, saboda haka za a fuskanci hukuncin da ya dace.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *