Kwamitin majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya sun soki yunkurin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa garin Maradi a jamhuriyar Nijar.

Jaridar Punch tace kwamitin hadaka na sufurin kasa da na ruwa a majalisar tarayya sun koka kan yadda za a gina bari biyu a dogon da zai fita daga kasar.

A lokacin da sauran titunan jirgin kasa da ke Najeriya suke da bari daya, wannan dogo da za a gina daga Kano zuwa Maradi zai zo ne da barin hanya biyu.

‘Yan majalisar sun fusata a lokacin da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya gabatar da abin da kasafin kudin shekara 2022 na ma’aikatarsa ya kunsa a jiya.

Ministan sufurin ya bayyana amfanin wannan gagarumin aiki, yace zai bunkasa kasuwanci a Afrika a lokacin da ake kukan an yi watsi da kudancin kasar.

“Gina titin jirgin kasan Najeriya zuwa Maradi (kasar Nijar) mai kilomita 284 zai taimaka wajen saukaka kasuwanci tsakanin kasashen yammacin Afrika.”

“Wannan gudumuwa da Najeriyaa za ta bada zai taimakawa dukkanin kasashen ta hanyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Nijar da Najeriya.” – Amaechi.

Shugabannin kwamitocin Sanata Danjuma Goje da Honarabul Pat Asadu sun ce ana kyale sauran bangarorin kasa a wajen ayyukan gina hanyoyin jirgin kasa.

Da yake bayani a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, 2021, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa an soma yin aikin gina titin jirgi daga garin Abuja zuwa Kaduna.