Featured Video Play Icon

Rashin halartar tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan taron kasa na Jam’iyyar PDP da aka kammala a karshen wannan makon, ya dada jefa shakku dangane da makomar sa, yayin da ake ci gaba da rade radin cewar zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni sun ce tsohon shugaban ya sanar da tafiyar sa zuwa Nairobi Kenya domin halartar taron tsaro da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka ta AU, sai dai wasu ‘yan jam’iyyar basu gamsu da uzurin da ya gabatar ba, inda suke cewa wani dalili ne kawai na kin halartar taron.

Jaridar Premium Times tace Gwamnan Bayelsa Douye Diri da takwaran sa na Oyo Oluseyi Makinde sun yi iya bakin kokarin su wajen janyo hankalin shugaban wdomin ganin ya halarci taron a ranar juma’ar da ta gabata amma hakar su bata cimma ruwa ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan dake zama babban Jakadan kungiyar ECOWAS a kokarin sasanta rikicin siyasar kasar Mali. © Presidency of Nigeria

Jaridar tace Gwamnonin biyu sun bayyana aniyar su ta samawa Jonathan wani jirgi na daban da zai kai shi Nairobi idan ya halarci taron na PDP amma tsohon shugaban yaki amincewa da bukatar su.

Premium Times ta nemi ji daga bakin mai magana da yawun Jonathan Ikechukwu Eze wanda ke tare da shi a Nairobi dangane da kin halartar taron amma kuma abin yaci tura.PUBLICITÉ