Kamfanin hamshakin attajirin Afirka Aliko Dangote ya sanar da rasuwar mataimakin shugaban rukunonin sa Alhaji Sani Dangote.

Dangote ya rasu ne a kasar Amurka ranar lahadi sakamakon rashin lafiyar da yayi fama da ita, kuma tuni jama’a suka fara aikewa da sakon ta’azziya ga ‘yan uwa da iyalan sa.

Sani Dangote yayi fice a bangaren aikin noma da harkokin man fetur da kuma bankuna, yayin da yake rike da mukaman shugabancin kamfanoni da dama dake karkashin rukunin kamfanin Dangote.

Mataimakin shugaban rukunin kamfanin Dangoten yayi kuma fice a bangaren wasan polo, abinda ya bashi damar zama shugaban kungiyar polo ta Najeriya da kuma ziyarar kasashe da dama wajen yin wasan cikin su harda Ingila da Argentina.

Daga cikin wadanda suka fara aikewa da sakon ta’azziyar su harda tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wanda ya bayyana shi a matsayin hamshakin ‘dan kasuwar da ya taimaka da dama wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya.