Wani rahoto da ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta fitar ya yi ikirarin cewa China na karfafa sashenta na makaman nukiliya cikin gaggawa fiye da yadda ake tsammani.

Rahoton ya ce China za ta iya mallakar makaman nukiliya 700 nan da shekarar 2027 kuma yawansu ya iya kai dubu guda nan da shekarar 2030 ninki biyu da rabi na hasashen da Amurka ta yi shekara guda baya.

China could have 700 deliverable nuclear warheads by 2027, and could top 1,000 by 2030 — an arsenal two-and-a-half times the size of what the Pentagon predicted only a year ago, according to the report.

Rahoton ya ce China na zuba makuden kudi a bangaren na ta na nukiliya inda ta ke karfafawa tare da fadada sashen ta hanyar samar da karin makaman nauikan na kasa da na ruwa da kuma na sararin samaniya.

Pentagon ta yi zargin yadda China ke ci gaba da gyaran sassan da za su taimaka mata kara karfi ta fuskar nukiliyar.

Rahoton ya ce Chinar kamar sauran manyan kasashe mafiya karfin nukiliya biyu Amurka da Rasha a shirye ta ke tsaf wajen aiwatar da manyan gwaje-gwajen makamai masu linzami mafiya hadari ta ruwa da iska da kuma karkashin kasa.