Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Amince Da Bayar Da Kaso 20 Cikin 100 Na Tallafin Kayayyakin Abinci Ga Cibiyoyin Addini Dana Gargajiya.

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa
shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da bayar da kaso 20 cikin 100 na
tallafin kayayyakin abinci ga cibiyoyin addini dana gargajiya.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a babban
taron tattaunawa na shugabannin addinai kan abinci mai gina jiki a Najeriya,
wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja
Shettima yace za’a saka makarantun tsangayu,cikin tsarin.
Mataimakin shugaban kasar yace gwamnati na aiwatar da dabaru ta hanyar
ma’aikatar noma ta tarayya domin ganin an aiwatar da shirin cikin sauki.
Shirin zai kasance karkashin ofishin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren
tattalin arziki, Sen. Abubakar Atiku Bagudu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *