Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarcibikin naɗin sabon Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru HaladuDanu.

Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci
bikin naɗin sabon Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru Haladu
Danu.

Tsohon shugaban ƙasar wanda ya kasance babban bako
na musamman na ɗaya daga cikin tawagar manyan baƙi
da ta haɗa da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim
Shettima da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf
Tuggar da suka halarci bikin naɗin a Masarautar Dutse da
ke Jihar Jigawa.
Rahoton ya Kara da cewa naɗin Nasiru Danu a matsayin
Sardaunan Dutse na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Dokta
Maitama Bello.
Kafin naɗin na yanzu, Alhaji Danu shi ne mai riƙe rawanin
Dan Amanar Dutse wanda tsohon Sarkin Dutse, Marigayi
Nuhu Muhammad Sanusi ya naɗa masa a ranar 4 ga watan
Mayun 2017.
Bayanai sun ce Alhaji Danu gogaggen ɗan siyasa kuma
fitaccen ɗan kasuwa da ke riƙe da jagorancin Kamfanin
Casiva Limited wanda ya assasa Gidauniyar Nasiru Danu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *