Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan ta’adda da yawa a Katsina da Zamfara

Dakarun rundunar sojojin Nijeriya sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindiga a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Faska da ke Katsina inda suka kashe guda takwas tare da ƙwato bindigogi uku ƙirar-gida, da kakin soji da hatsi mai yawa, a cewar sanarwar.
Sojojin Nijeriya sun yi nasarar far wa maɓoyar gawurtaccen ɗan ta’adda, Hassan Yantagwaye, a ƙaramar hukumar Tsafe
Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta’addanci a Katsina da Zamfara sun ka jerin samame a maɓoyar ƴan ta’adda inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin da safe.
Kazalika ta ce dakarunta sun kama tarin miyagun ƙwayoyi a hannun wasu masu fasa-ƙwauri a jihar Ogun da ke kudancin ƙasar.
Yantagwaye da tawagarsa ne suka yi garkuwa da mutane da dama tare ta’addanci a wasu yankuna Arewa Maso Yammacin Nijeriya. Yayin samamen, dakarun sun yi luguden wuta a kan ta’adda bayan sun yi musayar harbe-harbe, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da ƙwace makamai da dama,” in ji sanarwar.
Kazalika ranar 30 ga watan Maris, dakarun rundunar sojojin Nijeriya sun yi ba-ta-kashi da ƴan bindiga a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Faska da ke Katsina.
Haka kuma sojojin Nijeriya sun ce sun kai samame da daddare a wani yanki na ƙaramar hukumar Ohaukwu d ke jihar Ebonyi ranar 31 ga watan Maris inda suka gamu da mayaƙan ƙungiyar tsageru ta Effium.
Dakarun sun murƙushe tsagerun inda suka kama ɗaya daga cikinsu. Kazalika dakarun sun ƙwace bindiga samfurin AK – 47 da alburusai kuma “yanzu haka ana gudanar da bincike kan mutumin da aka kama.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *