Za mu sake nazari kan dakatarwar da muka yi wa Ningi – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Godswill Akpabio ya ce a kusa majalisa za ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi mai wakintar Bauchi ta tsakiya a jam’iyyar adawa ta PDP.
Hakan na zuwa ne ƙasa da awa 24 da ɗan majalisar ya aike wa Akpabio da wasiƙa wadda ciki ya yi masa barazanar ɗaukar matakin shari’a kan dakatarwar da aka yi masa idan ba a janye ta ba nan da mako guda.
An dakatar da Ningi ne bayan wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa wadda cikinta ya yi zargin cewa akwai naira tiriliyan sama da uku da aka cusa a cikin kasafin kuɗi ba tare da an yi bayanin me za a yi da ita ba.
Bayan wata doguwar muhawara da aka yi a majalisar mai kama da titsiye, an sanar da dakatar da Ningi watanni uku kuma an nemi ya rubuta wasikar neman afuwa saboda ‘ɓata wa majalisar suna da ya yi’ in ji Shugabanta.
Cikin wasiƙar da lauyan Ningi ya rubuta, Femi Falana ya ce Ningi ya zargi Akpabio da zama mai ƙara mai gabatar da ƙara kuma mai yanke hukunci duk shi daya, wanda hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *