Kungiyar kare hakkin dan adam ta IHRC-International Human Rights Commission ta shiga jerin masu bukatar majalisa ta sauya matsaya kan dakatar da Sanata Abdul Ningi.

IHRC ta kara karfafa matsayar da kungiyar raya dimokradiyya ta arewa karkashin Dokta Usman Bugaje ta yi a taron manema labaru.
Kungiyoyin sun nuna tasirin majalisa a tsarin dimokradiyya da ya dace ta zama fagen kare masu fadar albarkacin baki da ba da uzurin baiyyana hujja kafin daukar mataki.
Majalisar dai ta dakatar da Abdul Ningi na tsawon wata uku bayan zargin cushe da ya ce an yi a kasafin kudin bana.
Shugaban IHRC a Najeriya Ambasada Abdullahi Adamu Bako ya ce sun mika rahoton matsayarsu ga cibiyarsu ta duniya da ke nuna matakin na majalisa ya yi karar-tsaye ga tsarin dimokradiyya.
A nan IHRC ta bukaci janye dakatar da Sanata Ningi da majalisar ta yi don muradun sulhu.
Shi ma babban dattijon siyasa na NEPU Hussaini Gariko ya nuna takaicin matakin da majalisar ta dauka yana mai cewa “Za mu kafa ofisoshi a manyan biranen Najeriya don yada manufar nuna rashin dacewar irin wannan matakin.”
Shugaba Tinubu dai a liyafar shan ruwa na azumi da shugabannin majalisar ya musanta yin cushen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *