Yan bindiga sun hallaka sabon ango tare da tilasta wa matan aure karya azumin a jihar Neja.

’Yan bindiga sun harbe wani sabon ango yayin harin da suka ƙaddamar a kasuwar Madaka da ke Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja.

Angon wanda aka bayyana sunansa da Sani, na daga cikin mutum 21 da ’yan bindigar suka hallaka a kasuwar da manoma ke ci mako-mako a ranar Alhamis.

Bayanai sun ce angon wanda mahauci ne da ke zaune a garin Kagara na Karamar Hukumar Rafi, ya fita kasuwancin sa na sayar da nama lokacin da harin ya auku

Kazalika, ’yan bindigar da suka kai harin da tsakar rana sun tilasta wa mata musulmi karya azuminsu.

Mazauna yankin sun ce an ƙaddamar da harin ne da misalin ƙarfe 3 na yammacin ranar Alhamis lokacin da hada-hada a kasuwar ta ɗauki harama.

Wani mazaunin yankin mai suna Salihu Abdullahi, ya bayyana cewa ’yarsa mai kimanin shekaru takwas na cikin waɗanda ’yan bindigar suka harbe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *