Sakamakon Wasanni: Pillars ta doke Sporting Lagos, Gombe ta rike Doma

A cigaba da gasar ƙwallon ƙafa ajin kwararru, a fili wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, Kano Pillars tayi nasara akan Sporting Lagos da ci daya da nema a wasan mako na 37 na gasar da aka gabatar da yammacin ranar Asabar.

Pillars tayi nasara zura ƙwallon ta ne a daidai minti na 48 ta hannun dan wasan ta M. Umar kuma da wannan nasarar Kano Pillars ta koma kan matsayi na shida a jadawalin kungiyoyin dake fafatawa a wannan gasa da yawan maki 41 daga wasanni 27.

A filin wasan na Pantami dake jihar Gombe, an tashi wasa kunnen doki watau daya da daya tsakanin kungiyar Doma United da Gombe United.

Gombe United ce ta fara zura ƙwallon a raga Doma, ta hannun da wasan ta mai suna, D. C Naj a daidai minti na 12 na zangon farko yayin da ɗan wasa M. Usman ya farke wa Doma ƙwallon da aka zura ma ta a daidai minti na 64 na wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *