Ana cin mutuncinmu a shafukan sada zumunta – Fulani

A Najeriya, wata kungiyar dattawan Fulani ta duniya mai suna ”Tabital Pulaku International”, ta bayyana damuwa tare da Allah-wadai, da yadda ake amfani da shafukan sada zumunta ana yi wa al’ummar Fulani kudin goro wajen aibata su da cin zarafinsu da kuma daukar duk wani Bafulatani a matsayin mai aikata miyagun laifuka.
Kungiyar ta ce bai kamata hukumomi su zura ido suna kallo ana muzanta al’umma guda, sakamakon wasu bara-gurbi ‘yan kalilan da ke cikinta ba.
Kungiyar ta ce a yanzu an mayar da shafukan sada zumunta, wani dandali da ake yi wa al’ummar Fulani da shugabanninsu dukan ɗiyan kanya, ana zaginsu da cin mutuncinsu da yaɓa masu duk wasu bakaken maganganu.
Awwal Gonga, mataimakin shugaban reshen kungiyar a Najeriya, ya ce ana yin zage-zage da cin mutuncin Fulani a shafukan sada zumunta, amman kowa ya yi shiru a Najeriya, “a duniya ba a danganta laifi da ƙabilanci ko addini. “
Awwal Gonga ya ce Fulani ƙalilan ne ake samu da aikata laifi saboda haka bai kamata ana ma Fulani kudin goro ba, ‘kada a danganta kaifin mutum da ƙabilarsa kuma gwamnati ta yi aikinta.”
Gonga ya ce masu aikata miyagun laifukan nan, duk da kankantar yawansu a cikin al’ummar ta Fulani, tamfar cinnaku ne. Domin kuwa ba su san na gida ba, hatta su ma Fulani makiyayan ba su tsira daga hare-haren ‘yan bindigar ba.
Duk da yake dai kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba kowanne dan kasa damar fadar albarkacin bakinsa, amma Awwal Gonga na kungiyar dattawan Fulanin ta duniya, yana ganin akwai bukatar baki ya san abin da zai fada, don kada garin neman lada a rika ture kurtun alhaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *