Daniel Alves zai bar gidan Yari.

Mahaifin dan wasan gaban Brazil, Neymar ya fito fili ya nisanta kansa da raɗi-raɗin da akeyi na cewa zai biyar tarar da hukumomi a kasar Spaniya suka yi wa tsohon dan wasan Barcelona ɗan asalin ƙasar Brazil Daniel Avles wanda hukumomin kasar ke tuhuma da laifin cin zarafi wata mata.

Shi dai Daniel Alves ya samu kansa a tsaka mai wuya ne biyo bayan yadda wata kotu ta same shi da laifin cin zarafi wata mata kuma ta yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru huɗu da rabi ko kuma biyan tarar fam miliyan daya.

Ana sa ran tsohon ɗan wasan kulob din na PSG zai daukaka kara akan hukuncin, sai dai kuma ya gaza biyan kudin belin da kotun ta bukata kasancewar kotun ta ba da izinin rufe dukkanin asusun ajiyar da ya mallaka.

Batun cin zarafin mata dai na daya daga cikin matsalolin da fitattun yan wasan kwallon ƙafa ke fuskanta a kasashen turai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *