A nada Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta kasa ta nada tsohon dan wasan Super Eagles, Finidi George, a matsayin sabon kocin kungiyar ƙwallon ƙafa ta kasa na wuccin gadi.

Kungiyar ta Super Eagles dai ta kasance ba ta da mai horaswa tun bayan da ta yi sallama da mai horaswa ta da ƙasar Portugal Jose Peseiro, wanda shine ya jagoranci kungiyar kaiwa ga wasan karshen na cin kofin nahiyar Afrika da aka gabatar a kasar Ivory Coast.

Finidi George ya kasance mataimakin ga shi Jose Peseiro kuma ana sa ran zai jagoranci wasannin sada zumunta da kungiyar ta Super Eagles za ta gabatar a wannan watan na Maris da kasashen Ghana da kuma Mali.

Tuni dai sabon kocin na wuccin gadi wanda a yanzu haka ke da shekaru 52 da haihuwa ya kama aiki don ganin cewar kungiyar ta samu nasara a wasannin sa da zumunta da za ta fafata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *