FAIFAN BIDIYON DOLLAR – MUHUYI MAGAJI BASHI DA IKON BINCIKAR GANDUJE.

Babban Kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci cewar hukumar karbar korafe korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ba ta da hurumin BINCIKAR tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na rikon kwarya, Dr Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon karbar rashawa na Dalar Amurka da ake zargin yan kwangilar sun bashi.

Da ya ke yanke hukuncin, alkalin kotun mai Shari’a Abdullahi Liman, ya bayyana cewa laifin da ake zargin tsohon gwamnan da aikawa, laifin ni da ya shafi kasa, a don haka ministan shari’ar na kasa ko kuma hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ne kaɗai zasu yi gabatar da tuhuma ko bincike akan sa.

Sai dai kuma da ya ke jawabi bayan yanke hukuncin, lauya hukumar karbar korafe korafe ta jihar Kano, Usman Umar Fari, ya sha alwashin cewar zasu daukaka kara akan hukuncin kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *