Fitattacen jarumin barkwancin nan na Najeriya, Mr. Ibu ya riga mu gidan gaskiya

Fitattacen jarumin barkwancin nan da ke fitowa a fina finan Najeriya, John Okafor, wanda ka fi sani da Mr. Ibu ya riga mu gidan gaskiya.

Mr. Ibu ya rasu a ranar Asabar, a wani asibiti bayan ya sha fama da rashin lafiyar da yayi sanadiyar yanke masa kafa guda.

A yan kwanakin baya dai, iyalan jarumin sun fito sun bayyana wa duniya halin rashin lafiyar da mahaifinsu ke ciki tare da rokon yan Najeriya kan su kawo masa ɗauki.

Sai dai kuma bayan wasu daga cikin al’umma da kungiyoyi sun kai masa tallafi ne, sai aka samu labarin cewar daya daga cikin ya’yansa tayi awon gaba da gudummawar da aka tara masa.

Tuni dai al’umma wannan kasa da abokan aikin sa na Nollyhood ke aika sakon taaziyar su ga iyalan Mr. Ibu ta shafukan sada zumunta.

Za’a dau tsawon lokaci dai ana tunawa da barkwancin Mr. Ibu a fina finan Najeriya duba da kwarewar sa a wannan fannin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *