Tafiyar Mbappe zuwa Madrid na iya fuskantar cikas.

A wani lamari mai kama da zaman sulhu, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shirya liyafa cin abinci wanda ake san zai samu halarci ma mallakin kotun ga PSG, Nasser Al-Khelaifi da Sarkin Qatar, Tamim bin Hamad Al-Thani da kuma ɗan wasa gaba na kotun din PSG Kylian Mbappe.

Wannan liyafar na zuwa ne a daidai lokacin da shi ɗan wasa Kylian Mbappe ya bayyana aniyar sa na barin kungiyar ta PSG inda mazarta ke kyautata zaton yana da niyyar komawa kolub din Real Madrid.

A baya dai shugaban na kasar Faransa ya taka muhimmiyar rawa wajen hana Kylian Mbappe barin kungiyar ta PSG Kuma manazarta na kallon shirya liyafar a matsayin wata dama da za’a iya amfani da ita wajen jan hankalin dan wasan mai shekaru 25 canja tunanin sa na barin kasar Faransaa zuwa Spaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *