Fiye da shaguna 50 sun kone a wata kasuwa a jihar Kano

Sama da shaguna 50 ne suka kone kurmus sannan dukiyar miliyoyin Naira ta lalace a wata gobara da ta tashi a kasuwar ’yan Katako da ke unguwar Rijiyar Lemu a Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Shugaban kasuwar, Mamuda Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.

Ya ce shagunan da gobarar ta shafa na da katako, injin feshi, kujeru, da sauran kayan aikin kafinta a cikin su.

Sai dai ya yaba wa jami’an Hukumar Kashe Gobara ta jihar, bisa kai dauki a kan lokaci da suka yi zuwa kasuwar.

Kazalika, ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu hannu da shuni da su tallafa wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsu.

Har wa yau, kakakin hukumar kashe gobara na jihar, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *