Yara uku, yan gida daya sun rasa rayukan su sakamakon rufe kan su a mota.

Lamarin ya faru ne a gida mai lamba 8 dake kan titin Boluke a unguwar Zango-Kulende dake cikin garin Ilorin a jihar Kwara sakamakon rufe kansu da yaran suka yi a cikin motar da mahaifinsa ya karbo aro.

A cewar wandada lamarin ya afku a idanun su, sun bayyana cewa mahaifiyar yaran mai suna Shade Silifat, ta fita daga gidan a kokarinta na sayen abincin da za ta girkawa yaran bayan dawowar su daga makaranta yayin da yaran suka bude motar tare da shiga ciki domin yin wasa inda daga bisani suka kasa bude motar kuma rashin isasshen iska yayi sanadiyar galabaitar su.

Bayan mahaifiyar su ta fahimci halin da ya’yan nata ke cikin ta nemi taimako, inda aka garzaya da su zuwa asibitin Olutayo, inda daga nan kuma aka garzaya dasu zuwa asibitin kwararru na jami’ar Ilorin, a inda likitoci suka tabbatar da rasuwar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *