Wutar Lantarki Ta Dawo A Nijar Bayan Janye Takunkumin ECOWAS

Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.

An dage wasu takunkuman ne bayan wani taron kungiyar na musamman kan zaman lafiya da siyasa da kuma yanayin tsaro a yankin kasashen ECOWAS a ranar Asabar a Abuja.

Tun watan Agustan bara, Najeriya ta katse wutar lantarki a Nijar bayan juyin mulkin soja da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.

Wannan juyin mulkin da sojoji suka yi a karshen watan Yulin bara, ya fusata shugabannin kungiyar ECOWAS, inda suka yi barazaanr daukan matakin soji a kan kasar.

Amma daga bisani ECOWAS ta kakaba takunkumai kan Nijar, domin matsa mata lamba don maida kasar kan turbar dimokaradiyya cikin gaggawa tare da sakin shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa da sauran wadanda suke tsare da aka kama yayin juyin mulkin.

Bukatar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi na a janye takunkuman biyo bayan kiran da tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon ya yi, wanda hakan ya taimaka wajen saurin daukar matakin ECOWAS na neman dawo da kasashen uku na yankin da sojoji su ka kwace mulki.

Al’ummar Nijar da musamman ‘yan uwan su a arewacin Najeriya sun yi farin cikin matakin dawo da hasken wutar da rashinta ya jefa talakawa da dama cikin wahalhalun neman makamashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *