Hukumar kafafan sadarwa ta Rahma ta miƙa saƙon jajantawa ga karamar ministar babban birnin tarayya Abuja bisa ifitila’i gobara da ta samu.

Shugabar hukumar zartarwa ta tasoshin Rahma Radio da Talabijin Hajiya Binta Abdullahi Sarki Mukhtar ta aike da sakon jajantawa ga karamar ministar birnin tarayya Abuja Dr. Mariya Mahmud Bunkure bisa iftila’in gobara da ya faru a gidan ta dake birnin tarayya Abuja.

Cikin sakon jajen da ta aike a madadin hukumar zartarwa da gudanarwa na tasoshin biyu, Hajiya Binta ta bayyana lamarin a matsayin abin jajantawa wanda ta bukaci ministar da ta dauke shi a matsayin kaddara daga Allahu Subhanahu Wa Ta’ala.

Sakon wanda ke dauke da sa hannu shugaban sashin gudanarwa na tasoshin Rahma Radio da Talabijin Alhaji Salisu Idris Yakasai, Hajiya Binta ta nuna alhini da tausayawa bisa wannan iftal’ai, inda ta bukaci samun daukin Allah SWT game da asarar da akayi, da kuma addu’ar kare faruwar hakan anan gaba.

Gidan ministar wanda ke yankin unguwar Asokoro dake birnin tarayya Abujan, ya kama da wuta ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka tabbatar da cewa gobarar tayi gagarumar barna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *