An Samu asarar rayuka A Turereniyar Sayen Shinkafar Kwastam

A ƙalla Mutane bakwai, ciki har da mace mai juna biyu ake fargabar sun rasu a yayin turereniyar sayen shinkafar da Hukumar Kwastam ta yi gwanjo a kan N10,000 kowane karamin buhu a Jihar Legas.

Wasu da dama kuma sun jikkata a turereniyar da ta barke a lokacin da wasu bata-gari suka yi yunkurin shiga ofishin hukumar da ke gwajon shinkafar da karfin tuwo.

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da hukumar ta fara gwanjon shinkafar a ofisinta da ke yankin Yaba.

Gwanjon shinkafar da hukumar ke yi wani bangare na yunkurinta rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa da ake fama da ita fadin kasar.

Amma a martaninsa game da lamarin, kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce, “ba zan iya cewa an samu asarar rai ba, amma akwai wadanda suka sume kuma an kai su asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *