An ɗage sauraron Shari’ar Danbilki Kwamanda.

Wata Kotun Majistare a Jihar Kano, ta sanya ranar 22 ga watan Afrilu, 2024 domin sauraren karar da aka shigar da jigon jam’iyyar APC, Abdulmajid Danbilki Kwamanda.

An gurfanar da jigon na jam’iyyar APC, a ranar 23 ga watan Janairu, 2024.

Ana tuhumar da laifin tada tarzoma da kokarin tada hargitsi a Jihar Kano.

A baya dai Babbar kotun majistare ta Kano, ta tasa keyar Danbilki Kwamanda kan kalaman tunzuri bayan kalaman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso game da batun rushe masarautun jihar.

Wanda ake tuhumar dai ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Lauyan masu gabatar da kara, Barista Bashir Saleh, ya shaida wa kotun cewa ba su bai wa daya tsagin kwafin takardun karar ba.

“Muna neman afuwar wannan kotu mai girma da kuma sauran lauyoyi kan rashin ba su kwafin takardun saboda ba mu fassara ba.

“Amma ina tabbatar muku za mu yi hakan nan da kwanaki biyar.”

Ya kuma bukaci kotun da ta dage sauraron karar zuwa wani lokacin.

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, Tajuddeen Funsho, ya ce ya karbi uzurin lauyan amma bai amince da bukatar dage sauraron karar ba.

Alkalin kotun, Cif Majistare Abdulazeez Mahmud Habib, ya dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Afrilu, 2024 domin sauraren karar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *