Shugaban Senegal ya ce zai sauka daga kan mulki a watan Afrilu

Shugaban Senegal Macky Sall ya ce zai sauka daga shugabancin ƙasar a ƙarshen wa’adinsa a ranar 2 ga Afrilu, sai dai bai bayyana ranar da za a gudanar da zaɓen wanda zai gaje shi ba.

Mr Sall dai na fuskantar matsin lamba ya sanar da ranar zaɓen sabon shugaban ƙasa bayan yunƙurin ɗage zaɓen a farkon watan nan.

Matakin ya jefa Senegal cikin rudanin siyasa – ƙasar da ake ganin ta fi tsayuwa da ƙafarta ta fuskar dumokuradiyya a Afrika.

A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, Mr Sall ya gaza cika fatan al’ummar Senegal na saka ranar da za su kaɗa ƙuri’a kan wanda zai gaje shi.

Ya kuma yi alƙawarin ya sauka daga shugabanci bayan cikar wa’adin mulkinsa. A cewarsa, zai duba yiwuwar sakin ɗan hamayyar ƙasar Ousmane Sonko wanda tsare shi ya janyo zanga-zangar gama-gari a shekarar da ta gabata.

Mr Sall ya ce ba ya tunanin za a iya gudanar da zaɓe kafin 2 ga watan na Afrilu lokacin da ya tsara zai yi murabus.

Babu masaniya kan wanda zai jagoranci ƙasar na wucen gadi. Masu sukar Mr Sall sun zarge shi da ƙoƙarin ƙin sauka daga kan mulki. Akwai fargabar da ake cewa rikicin siyasa a Senegal na iya dagula lamura a yankin da ya sha fama da juyin mulki cikin shekara huɗu da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *