Gwamnan jihar Lagos ya ragewa ma’aikata kwanakin aiki daga kwanaki 5 zuwa 3

Gwamnatin Jihar Lagos da ke Najeriya ta ragewa ma’aikata ranakun zuwa aiki daga kwanaki biyar a mako zuwa kwanaki 3 a sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.

Yayin da yake jawabi, gwamnan jihar Sanwo Olu ya ce wannan mataki zai fara aiki ne kan kananan ma’aikata a mako mai zuwa yayin da ma’aikatan da ke kan mataki na 15 zuwa 17 zasu rika zuwa aiki kwanaki 4 a mako.

Dangane da tsadar rayuwa kuwa, gwamnan ya ce gwamnati zata bude wasu sabbin kasuwanni, inda ‘yan jihar zasu iya sayen kayan abinci a farashi mai rahusa.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin zata bude kasuwanni guda 42 a sassan jihar, wadanda zasu rika ci duk ranar Lahadi, inda kuma za’a rika sayar da kayan abinci da basu zarta naira dubu 25 ba.

Kari kan wannan kuma Sanwo Olu ya ce gwamnatinsa zata samar da wasu cibiyoyin rarraba abinci, wadanda za’a rika wuni ana rabawa marasa karfi dafaffen abinci, har zuwa lokacin da za’a sami dai-daituwar al’amurra.

Mr Olu ya kuma yiwa ‘yan jihar alkawarin ragin kaso 25 cikin 100 na kudin motar da ake biya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *