Dalilan da suka sa za mu binciki gwamnatin Buhari – Ndume

Majalisar Dattijan Najeriya ta bayyana dalilan da ya sa ta yanke shawarar binciken tsohuwar gwamnatin Buhari.

A zaman da ta yi ranar Talata ne majalisar ta tsayar da shawarar gudanar da bincike kan yadda tsohuwar gwamnatin ta kashe wasu kudi da suka kai tiriliyan 30 da ta karba daga Babban Bankin kasa CBN.

Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno kuma mai tsawatarwa na Majalisar Dattijan, ya ce ƴan majalisar na da damar yin bincike, kuma a cewarsa ” binciken zai soma ne daga CBN”

Ya kuma ce binciken na iya faɗaɗa ya kai har inda ba a yi tsammani ba.

Sanata Ndume ya ce za su bibiyi bayanai na wadanda aka ba kuɗin da kuma yadda aka kashe su da abin da aka yi da kudaden.

Ya ce binciken zai iya wuce tunanin mutane na za a binciki gwamnatin Buhari, “wataƙila abin ya wuce inda ake tsammani, kawai dai ba mu sani ba sai an yi binciken za a gane,” in ji shi.

Kuɗaɗen dai na bashi ne da Babban Bankin Najeriya ya ba gwamnati domin gudanar da ayyuka ko biyan wasu buƙatu.

Sanata Ndume ya ce sai bayan an karɓo kuɗaɗen kafin gwamnatin ta gabatar wa majalisa domin neman amincewarta, wanda ya ce ba ta da hurumi.

Majalisar dattijan ta yi iƙirarin cewa fitar da kuɗaɗen da su ba bisa ƙa’ida ba ƙarkashin jagorancin tsohon shugaban Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya jefa ƙasar cikin ƙarancin abinci da ta ke fuskanta.

Majalisar ta cimma matsayar kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudaden da ba a ba majalisar damar sanin haƙiƙanin yadda bayanan yadda aka kashe su ba.

Kwamitin zai kuma binciki naira tiliyan 10 na shirin tallafa wa manoma na Anchor Borrowers da kuma dala biliyan 2.4 daga dala biliyan bakwai na sauran shirye-shiryen gwamnati na tallafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *