Yansanda a Najeriya sun saki shugaban jam’iyyar LP da ta kama

Shugaban jam’iyyar LP Barista Julius Abure ya shake iskar yanci bayan sakin sa da rundanar yansanda tayi.

Da yake yiwa wasu daga cikin magoyan sa jawabi, Barr. Julius Abure, ya bayyana kamun da yansanda suka yi masa a matsayin wani mataki na.gwagwarmaya.

Sai dai kuma rundunar ta yansanda na cigaba da tsare shugaban reshen jam’iyyar na jihar Edo da sakataren yada labarai na jam’iyyar da kuma wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *