Yadda aka rufe kasuwar ‘yan chanji a Abuja

‘Yan kasuwar chanji da ke Abuja sun ce sun rufe kasuwar musayar kudin kasar waje da ke babban birnin kasar Abuja.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Abdullahi Abubakar Dauran ya shaida wa BBC cewa sun dauki matakin ne sakamakon yadda gwamnati ta bukaci hakan daga garesu.

A baya-bayan nan dai jami’an tsaron kasar sun yi ta kai samame kasuwar a wani yunkuri na dakile tashin farashin dala a kasar.

Shugaban ‘yan kasuwar ya ce a bangarensu sun yi biyayya ga umarnin gwamnati, domin yana da yakinin cewa gwamnatin ta yi hakan ne da kyakkyawar manufa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *