Issoufou ya musanta hannu a kifar da gwamnatin Bazoum

Tsohon shugaban jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou ya yanke shawarar shigar da ƙara a gaban kotu bayan zargin sa da aka yi da hannu a juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar bara.

Tsohon jakadan Faransa a Nijar ne ya yi wannan zargi sai dai lauyan Mahammadu Issoufou ya bayyana zargin a matsayin maganar da ba ta da tushe kuma wani yunƙuri na shafa masa kashin kaji.

Issoufou ya musanta zargin inda ya ce ganawar da Sylvain Itte ya ce ya yi da Tchiani ranar 28 ga watan Yuli, ba za ta zama hujjar zargin sa da hannu a juyin mulkin da aka yi a ƙasar ba.

Game da takun-saƙar da ake cewa akwai tsakanin shugaba Bazoum da Mahamadou Issoufou kan naɗin babban daraktan sabon kamfanin dillancin man fetur a kasar, lauyan na Issoufou ya ce zancen na ƙanzon kurege ne.

Lauyan ya kuma ƙara da cewa babu wata rashin jituwar da ke tsakanin ministan man fetur na ƙasar da Bazoum sai dai ma ra’ayinsu da ya zo ɗaya game da sabon kamfanin.

Lauyan ya kuma jaddada cewa Mahamadou Issofou ba shi da wata alaƙa da hamɓarar da gwamnatin da aka yi a don haka hujjojin da Sylvain Itte ya gabatar gaban hukumar tsaro ta ƙasa da kuma sojojin majalisar Faransa kawai yarfe ne.

A cewar lauyan, girman zarge-zargen da aka yi ne ya sa tsohon shugaban Nijar ɗin zai je kotu domin a yi masa adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *