Gwamnatin Benue ta bai wa baƙin makiyaya wa’adin mako biyu su fice daga jihar

Gwamnatin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, ta bai wa Fulani makiyaya da ta ce baki ne da ke kwarara cikin jihar da kuma ake zargin na dauke da makamai wa’adin makonni biyu su fice a jihar ko su fuskanci fushin hukuma.

Gwamnan jihar Hyacinth Alia ya kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da bin umurnin, sannan ya jaddada cewa har yanzu dokar nan da ta haramta kiwon dabbobi a sarari na ci gaba aiki.

To sai dai kungiyar Miyetti Allah reshen jihar ta nesanta kanta da ‘ya’yanta da yin kowane hadin gwiwa da dukan wasu bata garin makiya a cikin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *