Gwamnan Jihar Oyo ya karyata shugaban majalisar dattawan Najeriya

A wani abu mai kama da maida martani gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya ce babu kanshin gaskiya akan maganar da shugaban majalisar dattawa yayi na cewar gwamnatin tarayya ta bawa gwamnonin kasar nan naira biliyan talatin domin rage radaddin kuncin rayuwar da al’umma ke fuskanta.

Makinde wanda ya bayyana haka a yayin bikin bude masallachin Iseyin wanda gwamnatin sa ta gyara, ya bayyana cewa jihar sa ta Oyo ba ta karbi ko da sisi kobo ba daga gwamnatin tarayya ko wata hukuma ta tarayya da sunan tallafi.

Seyi Makinde wanda shine mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan, ya kara da cewa a matsayin sa gwamnan yana iyakan kokarin sa don ganin ya ragewa al’ummar jihar halin kun chin rayuwa da aka samu kai, ya kuma yi kira ga shugabanni a matakai dabam dabam da su kaucewa amfani da kalaman da zasu harzuka al’umma musamma ma a irin wannan hali na matsi da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *