Shugaban Senegal ya fara tattaunawa kan sabuwar ranar gudanar da zaɓe

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya fara tattauna da ƴan siyasa kan sabuwar ranar gudanar da zaɓen ƙasar, in ji jaridar Le Quotidien mai zaman kanta a yau.

Ƙasar dai ta faɗa cikin ruɗani bayan da shugaba Sall ya ɗage zaɓen da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu kafin babbar kotun ƙasar ta soke matakin tare da yin kira da a gudanar da zaɓen cikin gaggawa.

Shafin intanet na Seneweb ya ce ana sa ran shugaban na Senegal zai bayyana sabuwar rana nan ba da jimawa ba.

A halin da ake ciki kuma, ‘yar takarar shugaban kasa Rose Wardini wadda majalisar tsarin mulkin ƙasar ta wanke a watan Janairu duk da kasancewarta ‘yar kasar Senegal da Faransa ta fice daga zaben, kamar yadda shafin intanet ɗin ya ruwaito.

Batun Wardini na daga cikin batutuwan da shugaba Sall da jam’iyyar Demokradiyar Senegal (PDS) suka gabatar domin tabbatar da ɗage zaɓen har zuwa watan Disamba domin ba da damar gudanar da bincike kan tantance ‘yan takarar shugaban kasa.

Mummunar zanga-zangar da aka yi a Senegal ta sa Faransa da Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar Ecowas ta yammacin Afirka suka buƙaci Sall da ya mutunta shawarar majalisar tare da gudanar da zaɓe cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *