Issoufou na da hannu a cire Bazoum daga mulki – Tsohon jakadan Faransa

Tsohon jakadan Faransa a Nijar, Sylvain Itte ya shaida wa majalisar dokokin Faransa cewa tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou na da hannu kai tsaye wajen hamɓarar da gwamnatin shugaba Mohammed Bazoum.

A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, Itte ya yi zargin cewa shugaba Issoufou kodai ya kitsa juyin mulkin ko kuma ya goyi bayan hambarar da shugaba Bazoum, zargin da wani makusancin tsohon shugaban ƙasar ya musanta.

Tsohon jakadan na Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya yi wata ganawa ne ta sirri da ‘yan kwamitin da ke kula da harkokin tsaron kasar da kuma dakarunta a majalisar dokokin Faransa a Paris domin ba su bahasi kan abin da ya kai ga juyin mulkin da sojoji suka yi a a Nijar a shekarar da ta gabata.

A bayannin da tsohon jakadan ya yi wa ‘yan majalisar ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou, ya goyi bayan hambarar da mutumin da ya gaje shi Mohammed Bazoum saboda wani sabani da suka samu a tsakaninsu da ke da alaƙa da kuɗin mai na ƙasar.

Tsohon jakadan ya ce, Bazoum ya nuna turjiya wajen yarda ya nada dan Mohammadou Issoufou a matsayin shugaban sabon kamfanin mai na kasar a wanna lokaci da gwamnati ke sa ran samun bunkasa a yawan man da take samarwa.

Tun a watan Nuwamba na shekarar da ta wuce ne Itte ya gabatar da wannan jawanbi ga ‘yan kwamitin tsaron na majalisar dokokin ta Faransa amma sai a kwanan nan ne majalisar dokokin ta wallafa shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *