‘Ana kashe miliyoyin jakuna duk shekara don haɗa maganin gargajiya’

Wata ƙungiyar tallafi ta ƙiyasta cewa ana kashe kusan jakuna miliyan shida duk shekara domin biyan buƙatar maganin gargajiya na China.

Ƙungiyar mai suna Donkey Sanctuary, ta ce raguwar yawan jakuna a China ya tilasta wa masana’antar karkatar da hankalinta zuwa Afirka domin samun fatar jakunan da za a yi amfani da su wajen samar da sinadarin gelatine.

Hakan ya janyo ƙaruwar satar jakunan Afirka lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin jama’a da ke yankunan marasa galihu da ke dogara kan dabbobi wajen tafiyar da ayyukansu na karkara.

Yanayin ya tilasta wa ƙungiyar tarayyar Afirka tattauna yiwuwar sa dokar haramci kan kashe jakuna da kuma fitar da fatunsu a wani taro da za a yi ranar Asabar a Addis Ababa.

Afirka gida ne ga kashi biyu bisa uku na jakuna sama da miliyan hamsin a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *