Ɗage zaɓen Senegal ya ci karo da doka – Kotu

Kotun tsarin mulkin Senegal ta yanke hukuncin cewa ɗage zaɓen shugaban ƙasa zuwa watan Disamba da gwamnatin ƙasar ta yi ya saɓawa doka.

Kotun ta kuma yi watsi da ƙudurin da majalisar ƙasar ta amince da shi na ƙarawa shugaba Macky Sall wa’adin mulki.

Masu suka sun zargi shugaban da yunƙurin yin juyin mulki a ƙasar, da ake kallo a Afrika da ba a fiye yin juyin mulki ba.

Hukumomin yankin yammacin Afrika da na Tarayyar Turai sun bayyana damuwarsu kan jinkirta zaɓen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *