Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Oborevwori na Delta

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin kotun kararrakin zabe da ta daukaka kara da ya ayyana Sheriff Oborevwori a matsayin halastaccen gwamnan jihar Delta.

Kotun ta yi fatali da karar da dan takarar jam’iyyar APC, Ovie Omo Agege ya daukaka inda yake kalubalantar nasarar gwamnan jihar. A cewar kotun, karar ba ta da gamsassun hujjoji

Kotun ta ce mai karar ya gaza tabbatar da hujjojinsa na yin aringizon kuri’u da kuma saba dokokin zabe.

Tun farko, kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar gwamna Sheriff Oborevwori inda suka yi fatali da karar da Ovie Omo-Agege na jam’iyyar APC ya shigar.

Kotun kolin ta kuma yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar SDP ya shigar inda shi ma yake kalubalantar nasarar Oborevwori.

Kwamitin karkashin alkalai biyar ya yi watsi da karar saboda rashin cancanta.

Jam’iyyu uku – APC da SDP da LP, duka yan takarar suna kalubalantar matakin Inec na ayyana Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan Delta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *