Tinubu ya Jagoranci taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya na farko a 2024

Shugaba Tinubu ya Jagoranci taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya na farko a 2024

A halin yanzu Shugaba Bola Tinubu ya na Jagorantar taron Majalisar zartarwa ta tarayya a shekarar 2024.

Taron majalisar wanda ke gudana a fadar Shugaban ƙasa ta Villa a Abuja shine taro na farko da Majalisar zartaswar suka gudanar a shekarar 2024.

Kafin a fara taron Majalisar Ministocin, Shugaban kasar ya rantsar da Ambasada Desmond Akawor a matsayin sabon kwamishinan Gwamnatin tarayya na hukumar tattara kudaden shiga da kuma hukumar kasafin kudi mai wakiltar Jihar Rivers.

Ambasada Akawor ya maye gurbin Asondu Wenah Temple tsohon Kwamishinan Tarayya na hukumar daga Jihar Ribas wanda ya rasu kwanan nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *