Kano ta kafa kotun hukunta ’yan kwaya da masu kwacen waya

Kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi da kwacen waya a Jihar Kano ya kafa kotun tafi-da-gidanka domin gaggauta hukunta masu laifi.

Shugaban kwamitin, Birgediya Gambo Mai’Adua (mai ritaya) gargadi masu yi cewa du daina ko su gamu da fushin hukuma, domin gwamnatin jihar ba za ta lamuci ayyukansu ba.

“Kwamitin yana da kotun tafi-da-gidanka kuma yana da niyyar gyara dabi’un wadanda suka daina da kuma mayar da su cikin al’umma,” in ji shi

Gambo Mai’Adua ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan yakin da kwamitin ke yi na yaki da shan miyagun kwayoyi da satar waya a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *