Gobara tayi sanadiyar konewar shaguna 100 a kasuwar Panteka dake Kaduna

Akalla shaguna 100 ne suka kone a wata gobarar da ta tashi a tsakar dare a tsohuwar Kasuwar Panteka da ke garin Kaduna.

Ganau sun ce gobarar ta tashi ne kafin wayewar garin Laraba a Kasuwar Panteka da ke kusa da harabar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere (Kaduna Polytechnic).

Kasuwar Panteka wanda ke kusa da gidan gwamnatin jihar Kaduna a unguwar Tudun Wada, ta yi fice wajen kasuwancin kayan gini da karafa dangoginsu da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *