Tashin wani abin fashewa ya jefa mutane cikin fargaba a Ibadan

An ji wani kara mai karfi sakamakon tashin abin fashewa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahma fahimci cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 16 ga watan Janairu.

Kamar yadda aka ruwaito, an ji karar mai karfi kusa da yankunan Agbowo, Orogun da Bodija a garin.

Sai dai, a riga an gano musabbabin tashin abin fashewar ba a lokacin hada wannan rahoton.

Wani mazaunin Orogun, kusa da Jami’ar Ibadan (UI) ta fadawa jaridar mu cewa:

“Na gano cewa ya faru a harabar Domino Pizza a unguwar Bodijia. Ya girgiza unguwanni da dama a Ibadan.

Na kuma ji cewa ya lalata gine-gine masu yawa. “Mutane a Apete, Omi Adio, Mokola, sun ji girgizan fashewar.

” Wani majiya daban a Agbowo ya ce ya samu labarin cewa tukunyar gas ce ta fashe.

Kokarin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Adewale Osifeso, bai yi nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *