Tsohon Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya samo naira miliyan 50 daga kudin fansan ’yan Uwan Nabeeha

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Pantami, ya samo wanda zai biya miliyan 50 daga Naira miliyan 65 na kudin fansar sauran ’yan mata ’yan gida daya da ’yan bindiga suka sace a Abuja

Rahma ta ruwaito yaddaa daren Talata ’yan bindiga suka sace wani magidanci da ’ya’yansa mata shida a Karamar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya.

Daga bisani suka sako shi, suka nemi ya biya Naira miliyan 60 zuwa ranar Juma’a kafin su sako ’ya’yan nasa.

Zuwa ranar Juma’ar Naira miliyan 30 iyalan suka iya tarawa, amma ’yan ta’addan suka ki amincewa, suka kashe babbar ’yarsa, Nabeeha, wadda ke ajin karfe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *